Author: Kabiru Basiru Fulatan

Fitowar Dakta Chibuzo Okereke a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na Jam’iyyar Labour a zaɓen shekarar 2027 ta sake jawo muhawara kan makomar siyasa da shugabanci a Najeriya. A daidai lokacin da miliyoyin ’yan Najeriya ke fama da matsin tattalin arziki, rashin aikin yi, matsalolin tsaro da kuma tsadar rayuwa, ana sa ran jam’iyyun siyasa za su fito da sahihan manufofi da shugabannin da za su iya magance ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta. A cewar Jam’iyyar Labour, takarar Okereke na nuna jajircewarta wajen inganta adalci, riƙon amana da kuma shugabanci mai fifita muradun talakawa. Dakta Okereke, wanda ƙwararre ne a…

Read More

A yau, mutane da dama na kallon Jam’iyyar Labour Party a matsayin wata jam’iyya ta siyasa da wasu ’yan siyasa suka yi amfani da ita wajen samun farin jini ko cimma burinsu na siyasa. Sai dai idan aka yi nazari kan tarihinta, za a fahimci cewa asalin jam’iyyar ya sha bamban da yadda ake kallonta a yanzu. Labour Party ba ta samo asali daga tattaunawar masu ruwa da tsaki ko kuma yarjejeniyar manyan ’yan siyasa ba. A maimakon haka, ta samo tushe ne daga gwagwarmayar ma’aikatan Najeriya. A shekarar 2002 ne Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta kafa Jam’iyyar Party…

Read More

DAGA ABDULKARIM IBRAHIM A daidai lokacin da ake yawan jin rahotannin almundahana da karkatar da dukiyar jama’a daga wasu masu rike da mukaman gwamnati, wani mataki na gaskiya da rikon amana daga Jihar Kano ya jawo hankalin jama’a tare da sake tabbatar da cewa har yanzu akwai masu kishin amana a cikin hidimar gwamnati. Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano, Malam Mustapha Muhammad, ya samu yabo daga jama’a bayan ya mayar da Riyal 6,000 na Saudiyya, kwatankwacin kusan Naira miliyan 2.4, da aka yi masa kuskuren biyansa yayin rabon alawus-alawus ga ‘yan jaridar da suka halarci aikin Hajjin…

Read More

Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) reshen Jihar Kano ta yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa manufofinsa na kyautata jin daɗin ma’aikata, tare da yin kira da a ƙara tallafa wa masu karɓar fansho a jihar. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin saƙon taya murnar Babbar Sallah da shugaban riƙo na ƙungiyar, Kwamared Nura Rimin Gago, da sakataren riƙo, Kwamared Abbas Ibrahim suka sanyawa hannu. Yadda Cibiyoyin Farfesa Adamu Gwarzo Ke Samar Da Sabbin Damammaki Ga Matasan Afirka A cikin saƙon, NLC ta taya Gwamna Abba Kabir Yusuf, mataimakinsa Alhaji Murtala Sule Garo, ma’aikata, masu fansho da al’ummar Musulmi murnar…

Read More

Daga Musa Abdullahi Sufi A daidai lokacin da nahiyar Afirka ke neman shugabanni masu hangen nesa da za su kawo sauyi a fannonin ilimi, kirkire-kirkire, kasuwanci da ci gaban al’umma, sunan Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo na kara fitowa fili a matsayin daya daga cikin matasan da suka zamo abin koyi a nahiyar da ma duniya baki daya. Daga Arewacin Najeriya zuwa manyan cibiyoyin ilimi na duniya, Farfesa Gwarzo ya zama abin misali wajen jagoranci mai hangen nesa, bunkasa ilimi da kuma bai wa matasa damar cimma burinsu. Nasarorin da ya samu ba wai kawai na kansa ba ne, illa wata…

Read More

Kamfanin Maltina ya ƙaddamar da wani shiri na wayar da kan ɗalibai kan muhimmancin karatun kimiyya da fasaha a makarantu 30 da ke faɗin Jihar Kano, domin ƙarfafa harkar ilimi da bunƙasa makomar matasa a jihar. Wakilin kamfanin Maltina na Arewacin Najeriya, Kabiru Al-Kasim, ya bayyana cewa wannan ba shi ne karo na farko da kamfanin ke gudanar da irin wannan shiri a Kano ba, yana mai jaddada aniyar kamfanin na ci gaba da tallafa wa harkokin ilimi da ci gaban matasa. Da yake jawabi a wajen taron, Malam Sagiru Umar Dan Bare daga Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano, ya…

Read More

‎Dan takarar Majalisar Jiha a Karamar Hukumar Tarauni, Hon. Sagir Wada Sinkin Mai Iyali, ya bayyana godiyarsa ga al’ummar Jihar Kano bisa yadda suke ci gaba da nuna goyon baya da amincewa da tsarin jam’iyyar NDC Kwankwasiyya da kuma ‘yan takararta masu kishin kasa. ‎Hon. Sagir Wada Sinkin ya ce al’ummar Kano sun nuna cikakken goyon baya ga manufofin jam’iyyar tare da amincewa da shugabannin da suka hada da tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kuma jagoran siyasa, Peter Obi. ‎Rikicin KCSF: An Bukaci Hadin Kan Ƙungiyoyi Domin Kare Manufofin “Kano First” ‎Ya bayyana hakan ne yayin…

Read More

Daga Mohammed Bello Ana ci gaba da nuna damuwa kan rikicin shugabanci da ya kunno kai a cikin Dandalin Kungiyoyin Fararen Hula na Kano (KCSF), yayin da masu ruwa da tsaki ke gargadin cewa rikicin na iya kawo cikas ga manufar “Kano First” idan ba a magance shi cikin adalci da gaskiya ba. Wani masani kan bincike da tsara manufofi, Mohammed Bello, ya ce rikicin da ke cikin KCSF bai kamata a dauke shi a matsayin sabanin ra’ayi na cikin gida kawai ba, illa a kallesa a matsayin gwajin yadda kungiyar za ta iya kare martabarta da tsarin gudanarwarta. Bello,…

Read More

Daga Zainab Kamal Ibrahim Lalle na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin fitattun al’adun ado da suka yi tasiri a rayuwar Hausawa da sauran al’ummomin Musulmi, musamman a lokutan bukukuwa da shagulgula. Tun shekaru masu yawa da suka gabata, ana amfani da lalle a matsayin kayan kwalliya, tsafta da kuma nuna farin ciki a tsakanin mata Musulmi. Haka kuma, amfani da ita ya samu karɓuwa a Musulunci, inda malamai suka bayyana cewa addinin ya halatta amfani da ita cikin tsafta da ladabi. Rahotanni daga tarihin Musulunci sun nuna cewa tun a zamanin Annabi Muhammad (SAW), ana amfani da lalle…

Read More

Daga Zainab Kamal Ibrahim ‎ ‎Akalla mata 500 ne suka hallara a unguwar Gwammaja da ke karamar hukumar Dala a jihar Kano domin gudanar da saukar karatun Alƙur’ani mai girma tare da addu’o’in neman zaman lafiya da kawo ƙarshen ayyukan daba da kashe-kashen matasa da suka addabi yankin. ‎Jami’an EFCC Sun Kama Shugaban Hukumar Makamashi Kan Badaƙalar Naira Biliyan 500­ Shugabar ƙungiyar da ta shirya taron, Hajiya Halima Musa Abdullahi, ta bayyana cewa makasudin gudanar da taron shi ne neman taimakon Allah kan matsalar rashin tsaro da kashe-kashen da ake yi wa matasa marasa laifi. ‎Ta ce lamarin ya jefa…

Read More